Bikin Sallah a Kasar Hausa.
Bikin salla sabon abu ne a Ƙasar Hausa. Sabo ne da ma’ana ta cewa bikin salla ya shigo Ƙasar Hausa ne bayan shigowar addinin Musulunci. Wannan biki, jerin bukukuwa ne da ake gudanarwa a lokutan Idin Ƙaramar Salla da kuma Idin Babbar Salla.
Waɗannan bukukuwa da ake yi suna da yawa; akwai hawan salla da sarakuna ke yi da dawakai, akwai kuma bukukuwan da sauran jama’a ke yi waɗanda suka shafi kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, da gaishe-gaishe da kuma kyaututtuka da ziyarce-ziyarce.
Hawan sallah
Shi hawan salla biki ne da sarakuna ke gabatarwa. A Ƙasar Hausa, akan fara bikin hawan salla ne daga filin idi. Sarkin yanka yakan yi hawa da hakimansa da digantansa da sauran masu riƙe da muƙaman sarautar gargajiya.
Kowane ɗaya daga cikinsu zai hau dawakai da tawagarsa cikin kwalliya daga su har dawakan nasu, suna tafiya jama’a kuma na kewaye da su suna kallo suna miƙa gaisuwa. A ranar farko akan tashi daga filin idi zuwa gidan sarki. Idan aka je gidan sarki, sai a jira sarki ya zo ya sauka tukuna, sannan duk sauran hakimansa ɗaya-bayan-ɗaya su je su yi gaisuwa. Bayan an kammala kuma sai sarki ya yi jawabi ga jama’ar ƙasarsa baki ɗaya sannan a sallami kowa ya watse.
Idan aka gama wannan a ranar farko, to washegari kuma sai a ci gaba, wanda wannan yakan bambanta daga masarauta zuwa wata masarautar. Kowace masarauta akwai takamaiman wani guri da sarki ke zuwa a wannan rana, su kuma jama’a su fito gefen hanya suna miƙa gaisuwa ga sarki, fadawa kuma suna karɓa.
Sauran Bukukuwa
Daga cikin sauran bukukuwa da mutane kan yi a lokutan salla akwai kiɗan kalangu da ake yiwa ‘yan’mata suna rawa, akwai makaɗa da mawaƙa da suke gudanar da wasanni ciki har da makaɗan ban-dariya, da makaɗan jama’a.