Wasanni

Ronaldo zai zama na farko da zai buga Euro karo na shida

Cristiano Ronaldo zai zama na farko da zai buga gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro karo na shida a tarihi.

Portugal za ta yi wasan farko a rukuni na shida da Jamhuriyar Czech, inda ake sa ran Ronaldo zai buga wasan da zai kafa tarihi a Jamus Euro 2024.

Kawo yanzu dai dan wasan  mai rike da Ballon d’Or biyar ya yi wasa 25 jimilla da cin kwallo 14 a babbar gasar tamaula ta cin kofin nahiyar Turai.

Mai shekara 39 tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus ya lashe kofi daya da tawagar Portugal, shi ne Euro 2016.

Ronaldo ya fara buga Euro a karawar da Portugal ta yi da Girka, wanda ya ci kwallo a fafatawar ranar 12 ga watan Yunin 2004.

A Euro na Shekarar 2026, kyaftin tawagar Portugal ya yi kan-kan-kan da Michel Platini a yawan cin kwallaye da yawa a gasar mai tare raga.

Sai dai kuma a gasar  Euro na Shekarar 2020, Ronaldo ya haura tsohon dan wasan tawagar Faransa da cin kwallo biyar, jimilla da 14 ba wanda ya kai shi wannan bajintar.

Tuni kuma Ronaldo ya yi gasa biyar babu dan kwallon da ya buga Euro da yawa kamar shi, wanda ke fatan buga gasa ta shida a Euro na Shekarar 2024 a Jamus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button