Siyasa

Zamuyi dabarar da mukayi a Imo domin cin zaben Edo inji Gwamna Bassey Otu

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana aniyarta na samun karin gwamnonin jihohi a kudancin Najeriya nan gaba kadan Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a birnin Kalaba Bassey Otu ya fadi haka ne yayin da yake bayyana shirin da jam’iyyar ta yi domin fuskantar zaben jihar Edo da za a yi a gaba kaɗan.

Gwamnan na jihar Cross River ya ce yana da karfin gwiwa a kan cewa za su kara samun nasara a jihohin kudu musamman a jihar Edo da ake kokarin yin zaɓe.

Bassey Otu ya ce shi kadai ne gwamnan a jam’iyyar APC a yankin kudu maso kudu kuma ya gaji da zaman kaɗaici saboda haka za su yi kokarin samun karin jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button