Labaran Duniya
An Dage Lokacin Yanke Hukunci Kan Rikicin Sarautar Kano
A Yau Alhamis ne da misalin karfe 2 na rana ake saran yanke hukuncin masarautun kano
Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta dage lokacin da za ta yanke huklunci kan Rikicin Sarautar Kano da awa biyu.
Tun a farko dai kotun ta sanar da karfe 12 na ranar Alhamis a matsayin lokacin da za ta yi zama domin yanke hukunci.
Daga bisani, kafin cikar lokacin aka sanar da dage zaman da awa biyu zuwa karfe 2 na rana, inda sarakunan da ke shari’a kan Sarautar Kano za su san matsayinsu a gaban kotun.
Babbar Kotun Tarayya za ta yanke hukuncin ne kan dambarwar sabuwar dokar masarautun jihar, wadda ta tube Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da takwarorinsa na sabbin masarutu hudu da tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkira.