Siyasa

Dambarwar rikicin siyasa tsakanin tsohuwar Gwamnati da sabuwar Gwamnatin jihar  Kaduna sai Kara kaimi yakeyi

Wasu daga cikin tsofaffin kwamishinonin tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i, sun zargi Majalisar Dokokin jihar da shaci fadi, cikin rahoton da ta fitar na zargin tsohon gwamnan jihar da kwashe dukiyar al’umma.

Tsofaffin kwamishinonin sun ce an yi hakan ne da gayya, kana aka ƙi ba su damar bayyana a gaban kwamitin da aka kafa domin gudanar da wannan bincike domin su fayyace komi, a maimakon hakan ma sai aka tsaurara ƙa’idojin da aka sanya.

Jafaru Sani, yace wasu daga cikin basussukan da rohoton ya ce sun karɓo magana ce kawai ba a karɓa ba, kuma basu shiga asusun gwamnatin jihar Kaduna a zamanin mai gidan na su ba.

Yaqara da cewa basussukan da ake magana sun karɓo na kasashen waje sun ga kusan guda biyar, a ciki akwai na dala miliyan 280 don gina hanyoyi a karkara, bamu karɓi wannan ba, akwai kuma wani na dala miliyan150 na aikin gona a wani wuri na musamman, shima ko sisi ba a saka a asusun gwamnati ba” Inji Jafaru Sani.

Haka kuma, ya ce akwai wani bashi da kwamitin majalisar ya ambato na dala miliyan 130 da wata dala miliyan ɗari bakwai na mayar da yara da ke gararanba a tituna zuwa makaranta, sai wani na dala miliyan 20 da aka shirya amfani da su kan yadda za a farfaɗo da kiwon dabobi, dukkansu ba a ƙarbo su ba kuma babu ɗaya daga cikinsu da ya shiga asusun gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button