DA DAMI-DUMI: mahajjata 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia
Mahukunta a Saudi Arabia sun ce akalla mutum 1,301 ne suka rasu a yayin aikin Hajjin bana, kuma yawancinsu wadanda suka je ta barauniyar hanya ne da ke tafiyar kafa mai nisan gaske a cikin tsananin zafin da aka yi fama dashi a lokacin aikin Hajjin.
An gudanar da aikin Hajjin bana a cikin yanayi na tsananin zafi inda zafin a wasu lokuta kan zarta digiri 50 a ma’aunin selshiyos.
A cewar kamfanin dillancin labarai na SPA, fiye da rabin wadanda suka mutu ba su da cikakkun takardun da ke nuna cewa alhazai ne da suka je kasar ta Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana.Kuma wahala da tsananin zafi ne ke sanya su galabaita saboda basu da wajen fakewa ma’ana inda ake tanadarwa alhazai.
Kamfanin dillancin labaran y ace yawancin wadanda suka mutun tsofaffi ne ko kuma masu fama da wat acuta mai tsanani.
Ministan lafiya na kasar, Fahd Al-Jalajel, ya ce tuni aka dauki dukkan matakan da suka dace don wayarwa da jama’a kai a kan illoli da ke tattare da tsananin zafi da kuma yadda alhazan za su kiyaye.
Ya ce, an yi wa kusan mahajjata dubu 500 magani, ciki har da mutum fiye da dubu 140 da suka shiga kasar ta barauniyar hanya inda kuma har yanzu akwai wadanda ke kwance a asibiti suna karbar magani.
Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya rawaito jami’in diplomasiyya na cewa ‘yan kasar Masar 658 ne suka mutu.Sai Indonesia da ta ce ‘yan kasarta fiye da 200 ne suka mutu, yayin da India kuma ta ce adadin ‘yan kasarta da suka mutu a yayin aikin Hajjin bana saboda tsananin zafin sun kai 98.
Pakistan da Malaysia da Jordan da Iran da Senegal da Sudan da kuma Iraqi suma duk sun tabbatar da mutuwar alhazan nasu.
BBC Hausa