Labaran Duniya
Yadda ‘Yan Najeriya Suka Koma Lafto Bashi
Da alama matsin rayuwa da rashin isassun kudi a hannun jama’ar kasar nan ya sanya su juyawa kan karbar basussuka domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullun.
A cewar rahoton da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar ya nuna cewa an samu karuwar bashin da ‘yan Najeriya su ka karba a watan Janairu da 12% idan aka kwatanta da Disamban shekarar 2023.
Rahoton ya kara da cewa yanzu haka bashin da ake bin ‘yan Najeriya ya hau zuwa N3,028bn yayin da bankin CBN ya kara kudin ruwa kan rancen kudi da 26.95% a watan Mayu.