Labaran Duniya

Hukumar Yan Sanda Sun Kama Kansila Da Wasu Sarakunan Ƙauyuka Akan Satar Tiransifoma

Jami’an Rundunar ‘Yan sanda sun kama kansila da wasu sarakunan kauyuka uku akan  satar na’urar taransifoma a Jihar Gombe.

Premium Times ta ruwaito cewa Kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar  Gombe Buhari Abdullahi ne ya gabatar da waɗanda ake zargin a jiya Litinin.

Wanda ake zargi  Kansilan Abdullahi Panda mai wakiltar Kumo ta Unguwar Gabas dake ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe.

Sauran sun haɗa da Muhammad Majidadi mai shekara 40 wanda shi ne Hakimin Garin Majidadi, da Muhammed Sani mai shekara 43 wanda shi ne shugaban unguwar Sarkin Yaki da ke Kumo, da kuma Bello Ardo mai shekara 59 wanda shima yake rike da sarautar gargajiya.

Rahotanni na nuni da cewa A ranar 21 ga watan Yunin 2024 da misalin karfe 03:45 ne jami’an  ‘yan Sanda daga yankin Akko suka kama waɗanda ake zargi da sace tiransfomar kauyen Garin Majidadi wadda suka sayar wa Bello Ardo akan kuɗi naira Miliyan ɗaya da rabi 1.5.

Yace an ƙara kama sama da mutane 20 bisa zargin aikata laifu ka daban daban da suka haɗa da kisan kai, da fashi da makami da sauran laifuka a Jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button