Labaran Duniya

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Magantu Akan Kalaman Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu, ta yi kira ga Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima da ya riƙa gudanar da bincike kafin ya yi magana, akan duk wani labari da ya gani a kafafen sada zumunta.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Ofishin Sakataren yaɗa labaran gwamnan Jihar na Fazbuk a daren jiya, me ɗauke da sa hannun Sakataren Abubakar Bawa, inda sanarwar ta ce ba’a taɓa yunƙurin tsige Sarkin Musulmin ba, kuma bata taɓa yi masa barazanar hakan ba.

A cewar sanarwar “munyi zaton mataimakin shugaban ƙasa zai tuntuɓi Gwamnan Jihar sokoto kafin ya fito fili yayi magana akan batun tsige Sarkin Musulmin, domin kuwa ba mu taɓa tauye masa wani ‘yanci ko hakkinsa ba duba da yadda yake cin moriyar duk wani ikon da yake da shi.

Akan haka ne sanarwar gwamnatin jihar ta Sokoto, ta bawa ‘yan Najeriya tabbacin kare mutuncin Majalisar Sarkin Musulmin ta kowanne ɓangare kuma a kowanne lokaci.

A jiya ne Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima, ya gargaɗi Gwamnan Jihar Sokoto kan yunƙurin da yake yi na tsige Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku, bayan da Ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Musulmi (MURIC), ta zargi Gwamnan Jihar da yunƙurin tsige shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button