Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na daf da ɗaukar matashi Guiu daga Barcelona
Chelsea ta cimma yarjejeniya akan ɗaukar matashin ɗan wasan Barcelona Marc Guiu.
Ƙungiyar dai ta shirya tsaf domin gwada lafiyar ɗan wasan mai shekara 18 a birnin Landan.
An fahimci cewa Barcelona ta yi yunƙurin sauya saɗarar farashin matashin da ya kai fan miliyan biyar da ke ƙunshe cikin kwantaraginsa ta hanyar ba shi tayin sabon kwantaragi.
Guiu wanda ya fito daga kwalejin koyon ƙwallo ta Barcelona, ya ci wa kulob ɗin ƙwallo daƙiƙa 23 kacal da fara buga mata wasa, inda ta doke Athletic Bilbao a Shekarar 2023.
Ɗan wasan lamba tara ne mai hanzari amma kuma ba shi da ƙwarewa sosai ya ci ƙwallo biyu cikin wasa bakwai da ya buga zuwa yanzu.
Ana ganin Chelsea za ta saye shi ne don buga wa babbar tawagarta wasa amma kuma ana sa ran za ta ƙaro wasu ‘yan gaban a bana.
A dayan bangaren shi ma Omari Kellyman na Aston Villa mai shekara 18 na daf da komawa Stamford Bridge ɗin kan fan miliyan 19 kan yarjejeniyar shekara biyar bayan ya kammala gwajin lafiyarsa a makon nan.