Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Kasar Argentina ta tsallaka zagaye na biyu a Copa America
Argentina ta zama ƙasa ta farko da ta samu gurbin buga zagaye na biyu a gasar Copa America ta Shekarar 2024 da ke gudana a Amurka.
Tawagar ta samu nasarar kaiwa zagayen kwata fayinal ne sakamakon doke Chile 0-1 a wasan da suka buga da tsakar daren da ya gabata, bayan Lautaro Martinez ya ci ƙwallo a mintunan ƙarshe.
Argentina mai riƙe da kofin ta mamaye baki ɗayan wasan da aka buga a filin wasa na MetLife Sitadiyom dake birnin New Jersey, inda ta buga shot har 22.
Ɗan wasan gaba na Manchester City Julian Alvarez, da na tsakiyar Fiorentina Nicolas Gonzalez ne suka fara kai wa golan Chile Claudio Bravo hari tun da farkon wasan.