Labaran Duniya

Aikin Ginawa da Kuma Shata iyakar Kamaru da Najeriya mai kimanin tsawon kilomita dubu 2 ya zo ƙarshe

Bayan shafe shekaru 22, ana tattaunawa game da batun shata iyakar Kamaru da Najeriya, wadda ta taso daga tafkin Chadi har zuwa tsibirin Bakassi, mai tsawon kilomita dubu 2 da 100, ya zuwa yanzu dai an riga an kammala shata fiye da kilomita dubu 2 na iyakar tsakanin Kamaru da Najeriya wanda dama can akwai yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu.

A ranar Laraba ne Yaounde ta shirya karɓar wani taro na musamman na hukumar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, wanda ake fatan ƙarƙarewa a wannan Alhamis.

Taron da aka faro ranar Laraba a Otal ɗin Hilton da ke Yaounde, ƙarƙashin jagorancin wakili na musamman ga sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin yammacin Africa da Sahel, Leonardo Santos Simao, na da nufin yin nazari akan aikin shata iyakar, da kuma yadda za a taimakawa al’ummar da aikin ya biyo ta wurarensu.

Ministocin Kamaru da Najeriya Michel Zoah da Abdullateef Fagbemi ne ke jagorantar wakilan ƙasashen biyu.

Tun a watan Nuwamban shekarar 2001 ne aka kafa wannan Hukuma ta haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Kamaru, tsarin da sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya na wanncan lokaci, Kofi Annan ya assasa, bisa buƙatar shugabannin ƙasashen Paul Biya da Olusegun Obasanjo.

Aikin Hukumar shi ne tabbatar da an yi biyayya ga hukuncin da kotun duniya ta yanke a ranar 10 ga Oktoban 2002 kan taƙaddamar da ta taso tsakanin ƙasashen biyu game da mallakin iyakar, wadda a shekarar 2008, Najeriya ta mayar wa Kamaru a hukumance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button