Labaran Duniya

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Gwamnoni kan Mafi Karancin Albashi

Mataimakin shugaban kasar ne ya jagoranci taron da gwamnonin jihohi da mataimakan gwamnoni da ministoci kafin isowar shugaban kasar.

A yau Alhamis ne shugaban Najeriya Bola Tinubu da mataimakin sa Kassim Shettima suka gana da gwamnonin jihohi 36 na tarayyar kasar tare da ministoci, inda suka tattauna kan batun sabon mafi karancin albashin ma’aikata, da ma sauran batutuwan da suka shafi tattalin arziki.

Shugaban kasar da gwamnonin sun gana ne a taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) karo na 141, wanda ya gudana a zauren majalisar dokoki da ke Abuja, babban birnin kasar.

Taron na ranar Alhamis ya zo ne kimanin kwanaki biyu bayan da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi watsi da batun sake duba mafi karancin albashin ma’aikata.

A ranar Laraba ne gwamnonin karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) suka yi taro a Abuja inda suka tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago za su samar da ingantaccen albashi.

Idan za’a iya tunawa a jawabinsa na ranar dimokradiyya a ranar 12 ga watan Yunin 2024 Shugaba Tinubu ya tabbatar wa kungiyar kwadagon cewa nan ba da jimawa ba za a aika da wani kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button