Tinubu ya amince da bayar da tallafin N50,000 ga iyalai 100,000 a kowace jiha har wata uku
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da matakin bayar da tallafin naira dubu 50 ga iyalai dubu 100,000 a kowace jiha a faɗin ƙasar.
Shugaban ƙasar ya amince da matakin ne bayan tattaunawa da gwamnonin jihohin ƙasar a taron majalisar tattalin arziki ta ƙasa da ya gudana a fadar shugaban ƙasar ranar Alhamis
Shugaba Tinubu ya kuma amince da ware naira biliyan 155 domin sayen kayan abinci da za a raba a jihohin ƙasar domin rage masu raɗaɗi.
Haka kuma taron ya amince da fara aikin babban titin Sokoto zuwa Badagry da zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma jihar Legas.
Sannan kuma da ci gaba da aikin babban titin bakin teku da ya tashi daga Legas zuwa Calabar, wanda tuni aka fara gina shi.
Haka kuma Shugaban ya amince da gina layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da zai ratsa jihohin Rivers da Abia a Enugu da Benue da Nasarawa da Plateau da Bauchi da Gombeda Yobe da kuma jihar Borno.
Sannan da na Legas zuwa Kano da shi ma zai ratsa jihohin Lagos da Ogun da Oyo da Osun da Kwara da Neja da birnin Abuja da Kaduna da kuma jihar Kano.
Haka kuma taron ya amince da bai wa jihohin ƙasar haɗe da birnin Abuja naira biliyan 10 domin sayen motocin fasinja masu amfani da man CNG.