Labaran Duniya

Wata Kotun Shari’ar musulunci a kano ta daure mutumin da ya ke turawa matar aure fina-finan batsa ta WhatsApp.

Kotun shari’ar addinin musulinci mai namba 2, dake zaman ta a kofar kudu gidan sarki, ta yanke wa wani matashi hukuncin daurin watanni shida a gidan gyaran hali da tarbiya sakamakon samun sa da laifin lallashin Matar aure.

Mutumin mai suna Inusa Adamu Idris, mai shekaru 36, Mazaunin Unguwar Kawo a jahar Kano.

An gurfanar da shi bisa zargin lallashin Matar aure, Wanda hakan ya Saba wa sashi na 389 na kundin penel code.

Mai gabatar da Kara, Detective Aliyu Abideen, ya karanto masa hukunchin tuhumar da ake Yi masa inda nan ta ke ya amsa laifinsa, kan cewar tabbas ya na lallashin Matar aure ta hanyar tura Mata fina-finan batsa da yake Yi , tare da sanya ta a wani group da ake dora fina-finan batsa.

Shi dai wannan mutumin ya samu nambar Matar ne bayan ta Kai masa gyaran keken dinki da ya ke Yi Mata.

Matar auren ta Fara sanar da Mijin ta kan kalaman batsa da kuma fina-finan da ya ke turo Mata, Wanda daga bisani mijni ya garzaya sashin binciken manyan laifuka na yan sanda, inda aka kamoshi.

Bayan ya amsa laifinsa, mai gabatar da Kara Aliyu Abideen, yayi roko karkashin sashi na 350 da 356 karamin kashi na biyu na kundin ACJL 2019, tare da Neman alfarmar kotun ta yanke masa hukuncin nan ta ke, tunda bai musanta zargin da ake yimasa ba.

Alkalin kotun mai Shari’a, Isah Rabi’u Gaya, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida, a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya ko zabin biyan tarar naira dubu talatin ga gwamnatin jahar Kano.

Kotun taja hankalinsa tare da yi masa iyaka da Matar auren bayan an goge dukkanin abubuwan da ya tura Mata.

An kuma cike musu form na zaman lafiya bashi ba Matar magidancin da ya kawo korafin har tsawon shekaru 10, ba tare da wani ya ci zarafin wani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button