Labaran Duniya

Hare-haren yan Bindiga na Kara  zafafa a birnin Gwari

Yayin da masana ke gargadin samun ƙarancin abinci a bana a Najeriya, manoman da ke zaune a yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna, na bayyana damuwar su game da yadda ake samun ƙaruwar yawan hare haren da yan bindiga musamman a kan manoma.

Wasu daga cikin manoman da ke yankin sun ce al’amarni ya sa da yawansu sun daina zuwa gona sun koma zaman gida, inda ake ganin cewa lamarin  zai iya ƙara munana matsalar ƙarancin abinci wanda yanzu haka ake fama da shi a Kasar ta Najeriya baki daya.

Wannnan na faruwa ne a dai dai lokacin da damana ke kankama a arewacin Najeriya, lokacin da ya kamata manoman su dukufa wajen shuka, sai dai wani daga cikin monoman yankin ya shaida wa manema labarai cewa ‘A cikin sati biyun da suka gabata a kullum sai sun dauki mutane, kama daga kauyukan Randagi, da Kakangi, da Dagara, da Rema, da Bugai, a kullum haka muke fama, abin ya wuce dukkan yadda ake tunani” in ji shi.

Shi ma wani manomi ya ce a baya a baya jama’ar garuruwan na yankin Birnin Gwari sun sha yin sulhu tare da kulla yarjejeniya da ‘yan bindigar don su bar su su yi noma, amma sai daga baya su saba Kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button