Jam’iyar Democrat na tunanin Chanza shugaba Biden a matsayin ɗan takarar ta
Muhawarar farko ta yan takarar shugaban Amurka tsakanin shugaba Biden da Donald Trump ta kare, yayin da shugaba Biden ya bayyana cikin alamun rudewa, yana rawar murya, a wasu lokutan ma yana kasa ƙarasa magana.
Akalla an shafe awa daya da rabi ana tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasar da siyasar duniya, kuma miliyoyin mutane daga ciki da wajen Amurka sun kashe kwarkwatar idanunsu.
Tsohon shugaban kasarDonald Trump ya zillewa tambayar da aka yi masa kan hannu a karya dokar da wasu magoya bayansa suka yi ranar 6 ga watan Janairun 2021 lokacin da majalisun dokokin kasar ke tattara bayanan nasarar Biden.
A yayin mahawara yan takarar shugaban ƙasar Amurka, da aka tambayi Donald Trump ko zai amince da bukatun Putin wajen kawo ƙarshen yaƙin da yake da Ukraine da suka hada da barwa Rasha yankunan Ukraine da Rashar ta kwace ?, sai ya ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Sai dai Trump yace zai tabbatar na daidaita tsakanin Putin da Zalensikey, kafin ya karɓi rantsuwa a ranar 20 ga watan Janairun mai zuwa, zai Kuma kawo ƙarshen wannan yaƙi da ake yi, ana kashe mutane ba ƙaƙautawa, kuma zai samar da daidaito cikin hanzari kafin ya shiga ofishin shugaban ƙasa”
Shugaban ƙasar Joe Biden ya bayyana Trumph a mastayin wanda kotu ta kama da babban laifi:
Inda yace mutumin da ke tsaye da ni a nan mai laifi ne, kotu ta same shi da aikata babban laifi, kuma abin da ya ke faɗa a nan ko kaɗan babu gaskiya a cikinsa.
Sai dai Trump ya mayar masa martani da cewa ai shima dansa Hunter Biden kotu ta kama shi da laifin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
Mutanen biyu dai sun yi ta musayar bakaƙen maganganu a tsakaninsu, inda suke zargin juna da rashin katabus a mulkinsu.
Batutuwan da suka fi jan hankali a muhawarar sune baƙin haure, kiwon lafiya, zubar da ciki da kuma yaƙe yaƙen da ake fama da su a duniya.