Labaran Duniya

Kasar Faransa za ta samar da runduna ta musamman mai kula da nahiyar Afrika

Hukumomin Faransa sun baiwa Janar Pascal Ianni mukamin Shugaban rundunar Afrika da za ta fara aiki daga watan Agusta na wannan shekara.

Faransa kamar dai  Amurka da ta samar da runduna ta Africom da aka samar a shekara ta 2008, ofishin tsaron kasar Faransa ta duba yiyuwar samar da wata runduna da zata yi aiki a nahiyar Afirka da sunan kare martabar kasar ta Faransa.

Faransa za ta kafa wannan rundunar ta Afirka, kamar yadda sojojin Amurka suka yi na tsawon lokaci.

Matakin na Faransa na zuwa ne a wani lokaci da galibin sojojin na Faransa suka fice da cikin wasu kasashen da suka hada da Nijar,Burkina Faso,da Mali,wanda ake kalo a matsayin koma bayan gaske.

Ana kuma kyautata tsarin zais amar da sojoji kusan 600 a nan gaba, a wani lokaci da a shekaru biyu da suka gabata, baya ga wasu dakaru 1,600 da aka jibge a yammacin Afirka da Gabon, Faransa na da sojoji fiye da 5,000 a yankin Sahel a wani bangare na yaki da ta’addanci karkashin tsarin  Barkhane, kafin daga bisani sojojin Nijar,Burkina Faso da Mali bayan juyin mulki suka bukaci sojojin Faransa su fice daga kasashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button