Labaran Duniya
ASUU Ta Fara Shirin Shiga Yajin Aiki, Inda ta Gargadi Gwamnatin Tarayya
Ƙungiyar malaman jami’a ta Najeriya (ASUU) ta nemi gwamnatin tarayya da ta cika mata buƙatun da take nema a wajenta.
Ƙungiyar dai tayi barazanar cewa za ta shiga yajin aiki nan da makonni biyu idan har ba a cika mata buƙatun ta ba, inda ta koka kan yadda ba a sauyawa malaman jami’a albashinsu ba a cikin shekara 15 da suka gabata a ƙasar nan.