Jami’an Sojin Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da sace ƙarafunan layin dogo
Rundunar sojin Najeriya da ke aiki da runduna ta ɗaya dake jihar Kaduna sun kama akalla mutum 47 bisa zargin ɓarnatar da layin dogo.
Mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, Laftanar Kanar Musa Yahaya ne ya bayyana hakan yau Assabar a Kaduna.
Laftanar Kanar Yahaya ya ce dakarun rundunar sun kama mutanen ne a lokacin wani samame da suka kai unguwannin Kakau, Daji, da Anguwan Ayaba da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun na jihar Kaduna, ranar 26 ga watan Yuni.
Ya ce an kama mutanen ne lokacin da suka loda mota biyu na ƙarafunan layin dogon da suka sace.
Jami’in sojin ya ce waɗanda ake zargin sun bayyana wa sojojin cewa wani mutum ne mai suna Alhaji Babawo ke sanya su aikin sace ƙarafunan.
Kasar ta Najeriya wadda a baya bayan nan ke ƙoƙarin farfaɗo da sufurin jiragen ƙasa tana fama da matsalolin sufurin jiragen, inda a lokuta da dama wasu mutane ke ɓarnatar da titin jirgin ta hanyar sace ƙarafunan.