Kungiyar Kwadago A Najeriya tace Akwai Yiyuwar Gwamnoni basu fahimci dokar mafi ƙarancin albashi ba
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, ta mayarwa da wasu gwamnomin jihohin ƙasar martani kan ƙoƙarin da suke na ganin an bai wa kowacce jiha damar yanke abin da za ta iya biya a mastayin albashi mafi ƙaranci, saɓanin ƙokarin da ake yi na ganin an amince da farashi na bai ɗaya.
Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana cewar da alama gwamnonin ba su fahimci tsari da dokar albashi mafi ƙanƙancin ba.
Kwamared Benjamin Anthony, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriya, ya shaida wa Manema Labarai cewar albashi mafi ƙanƙanata ake son a biya, wanda kuma a duniya ma idan aka kayyade albashin mafi ƙaranci da za a biya, babu wani sashe ko jiha da za ta biya ƙasa da yadda aka ƙayade, tunda doka ce ta bai ɗaya, wadda ita kanta ƙungiyar ƙwadago ta duniya ta amince da ita.
Benjamin Anthony, ya kara da cewar “rashin adalci ne da ake fama da shi a kasar, a ce ga gaskiyar abin da tattalin arziki ke cewa, a ce ga albashi mafi karanci da za a biya, amma a ce ba za’ayi ba, ko da gwamnati ta ce zata bayar da naira dubu sittin da biyu (N62, 000) mun yi tambayar nawa ne kudin mai a ciki ?, nawa ne kudin mota nawa ne kudin makaranatar yara?, nawa ne kudin haya? inji shi.
Ya Kuma ja hankalin gwamnoni da ita kanta gwamnatin tarayyar Najeriya da cewar akwai bukatar su duba halin da yan kasar ke ciki, da ya sa suka bukaci mafi karancin albashi na naira dubu ɗari biyu da hamsin, wanda suka ce a hakan ma ba lallai ta biya buƙatar da ake so ba.
“ Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, sun ce za su biya dubu stittin da biyu, mu kuma mun ce sai dubu dari Biyu da hamsin, idan ka lura yanzu nawa ne kudin buhun shinkafa? Ya kai wajen Naira dubu Taminin to kaga kenan albashin da ake cewa za a biya mafi karanci ba ma zai iya saya wa ma’aikaci ko rabin buhun shinkafa ba.
Yanzu haka dai magana na hannun shugaban ƙasar Najeriyar Bola Ahmed Tinubu, don haka kungiyar ta ce tana jiran ta ga matakin da zai ɗauka, wanda daga nan za su fitar da tasu mastayar.
Maratanin ƙungiyar ƙwadagon ta Najeriyar na zuwa ne, bayan da wasu daga cikin gwamnonin jihohin ƙasar ke cewar ba za su iya biyan ko da Naira dubu 60 ko dubu 62 da gwamantin ƙasar ta yi wa ƴan ƙwadagon tayi ba a msatyin albashi mafi karanci.
Sai dai wasu daga cikin gwamnonin ƙasar irin su na Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar Gwamna Nasiru Idris Ƙauran Gwandu ya ce a shirye yake da ya biya ko nawa aka amince dashi a mastayin mafi ƙarancin albashin.