Asibitocin Gaza za su daina aiki nan da awa 24 saboda rashin fetur
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta yi gargaɗi kan cewa asibitocin birnin za su daina aiki na da sa’o’i 48 sakamakon rashin man fetur.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta yi gargaɗi kan cewa “sauran asibitoci da cibiyoyin lafiya da cibiyiyoyin samar da oxygen za su daina aiki nan da sa’i’o’i 48.”
Ma’aikatar ta ce sakamakon hana shigar da man fetur cikin birnin wanda da shi janaretocin asibitocin ke aiki, shi ya janyo hakan.
Baya ga man fetur, kayan abinci da magunguna na daga cikin ababen da Isra’ila ta saka takunkumin hana shiga da su Gaza.
Harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai da sanyin safiyar Lahadi sun kashe Falasdinawa bakwai tare da jikkata wasu da dama a Gaza.
Hare-haren sun faɗa kan gidaje a Rafah da birnin Gaza, inda aka samu asarar rayukan fararen hula da suka haɗa da kananan yara kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito.
Haka kuma makaman atilari sun yi luguden wuta a kudancin Rafah da tsakiyar Gaza, da kuma a birane da ke gabashin Khan Yunis. A unguwar Daraj da ke Gaza, farar hula ɗaya ya rasu da dama kuma sun jikkata a wani hari da sojojin na Isra’ila suka kai wani gida.
Masu shiga tsakani daga Amurka, Turai da ƙasashen Larabawa sun ƙara ƙaimi wajen ganin an kauce wa shiga gagarumin yaƙi tsakanin Isra’ila da mayaƙan Hezbollah na ƙasar Lebanon waɗanda ke samun goyon bayan Iran, suna masu fargabar watsuwarsa zuwa sauran sassan Gabas ta Tsakiya kamar yadda aka yi hasashe watanni da dama da suka wuce.
Iran da Isra’ila sun yi musayar yawu ranar Asabar sannan Iran ta ce yaƙin da za a yi zai kasance mai matuƙar muni.
Yanzu dai babu tabbas game da tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza, wanda hakan ne kawai zai sa Hezbollah da sauran ƙungiyoyi da Iran take mara wa baya su sauƙaƙa shirinsu na gwabza yaƙi da Isra’ila.
Ganin cewa babu ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta, jami’an diflomasiyya na Amurka da sauran ƙawayenta sun gargaɗi Hezbollah game da far wa Isra’ila da yaƙi.