Labaran Duniya
Akwai Yiyuwar Dauke Wutar Lantarki na kimanin tsawon Watanni Biyu a wasu Jihohin Najeriya
Za a dauke wutar lantarki na tsawon watanni biyu a wasu jihohin Najeriya
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya ya sanar da shirin gudanar da wani gagarumin gyara a layin rarraba wuta na Akure Osogbo mai karfin 132kV.
Wani rahoton na cewa gyaran wutar zai kawo cikas ga wutar lantarki a jihohin Ondo da Ekiti na tsawon watanni biyu.
A wata sanarwar da kamfanin wutar ya fitar ya kara da cewa jihohin da abin ya shafa za su fuskanci matsalar wutar lantarki da za ta dauki tsawon sa’o’i tara a kullum, daga ranar Litinin 1 ga watan Yuli zuwa 31 ga watan Agusta.