Labaran Duniya

Gwamnatin Tarayya ta Aika da tawagar ta a jihar Borno domin jajantawa ga wadanda harin Bom ya rutsa dasu

Wata Tawaga Da Shugaba Bola Tinubu Ya Aika Ta Isa Maiduguri Domin Jajanta wa Wadanda Harin Kunar Bakin Wake Ya Rutsa da su a Garin Gwoza.

Tawagar, karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ta mika sakon ta’aziyyar shugaban kasar ga gwamnatin jihar Borno da al’ummar Gwoza, har ma Mataimakin shugaban kasar ya bayar da gudummawar kudade ga wadanda abin ya shafa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Sanata Shettima ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da muni.
A cewar Shettima, Zuciyar Shugaban Kasa na tare da iyalan mutane 32 da suka rasa rayukansu a harin, da kuma wasu 42 suka jikkata, haka ma sauran mutane 14 da aka sallama daga asibiti.

Shugaban ya lashi takobin kawo karshen ta’addanci a Najeriya da kuma sauke nauyin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasar kamar yadda ya dauki Alkawari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button