Kungiyar kwallon kafa ta Kasar Portugal ta kai kwata fainal da ƙyar da gumin goshi a Euro 2024
Portugal ta kai matakin wasar daf da na kusa da na karshe, bayan da ta yi nasara a kan Slovenia da ci 3-0 a bugun fenariti ranar Litinin a Euro 2024.
Tun farko tawagogin sun tashi ba ci a minti na 90 da suka fafata, daga nan aka ƙara musu minti 30, nan ma ba a fitar da gwani ba.
Mai tsaron ragar Portugal, Diego Costa ne ya tare ƙwallo ukun da ta hada da ta Josip Ilicic da Jure Balkovec da kuma ta Benjamin Verbic
A cikin karin lokaci Cristiano Ronaldo ya ɓarar da bugun fenariti, to sai dai tsohon ɗan ƙwallon Manchester United da Real Madrida Juventus ya sharɓi kuka.
An kuma bai wa kociyan Slovenia, Matjaz Kek jan kati a wasan a karin lokaci.
Da wannan sakamakon Portugal, za ta fuskanci Faransa a zagayen daf da na kusa da na karshe ranar Juma’a.
Faransa ta kai gurbin kwata fainal, bayan da ta ci Belgium 1-0 ranar Litinin.
Wannan shi ne karo na biyu da suka fafata a tsakaninsu, inda Slovenia ta doke Portugal 2-0 a wasan sada zumunta a watan Maris a Ljubljana.
Har yanzu Slovenia ba ta taɓa cin wasa ba a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro a tarihi.
A Euro 2000 ta yi ban kwana a zagayen cikin rukuni da maki biyu, wadda a bana ta yi canjaras uku ta kare a mataki na uku.
Wasa ɗaya Slovenia ta taɓa yin nasara a babbar gasar tamaula, shi ne 1-0 da ta ci Algeria a gasar cin kofin duniya a 2010.
Slovenia ɗaya ce daga ƙungiyoyin da suka yi canjaras uku a karawar cikin rukuni a tarihin gasar cin kofin nahiyar Turai.
Portugal ta taɓa yin haka a Euro 2016, wadda ta kare a mataki na uku da maki uku, amma ta kai ga lashe kofin,
Haka itama Denmark canjaras uku ta yi a bana a Euro 2024 kamar yadda Slovenia ta yi a Jamus.