Shugaban Kasar Amurka Joe Biden na ci gaba da shan matsin lamba kan ya haƙura da takara
Shugaba Biden na Amurka ya dora alhaki a kan gajiya da kuma tarin tafiye-tafiye da cewa suna suka sa shi kasa tabuka wani abin a zo a gani a muhawarar da suka yi a makon da ya wuce da Donald Trump.
Ya bayyana wa masu bayar da tallafi a zaben da cewa kadan ya rage da bacci ya dauke shi a wajen muhawarar.
Mista Biden na wannan magana ne yayin da yake ta samun matsin lamba daga cikin jam’iyyarsa, Democrat kan ya sauka daga takarar zaben na watan Nuwamba.
Shugaba Biden mai shekara 81, ya ta’allaka, abin da wasu daga cikin jamiyyar tasa da ma wajenta ke cewa ya yi tsufan da ba zai iya kai jam’iyyar gaci ba a zaben shugaban kasar na watan Nuwamba da abokin hamayyarsa Donald Trump na Republican, ganin yadda a wannan muhawara ya gaza, da abin da ya ce gajiya ta inna-naha, saboda tarin tafiye-tafiye.
To amma na ganin wannan bayani kusan ba zai sa masu neman ya ajiye takarar ya bai wa wani ba, su gamsu, musamman ma ganin yadda a karon farko wani kusa daga jamiyyarsu ya fito fili ya ce ya hakura da takarar bisa nuna shakku ga yanayin lafiyar kwakwalwarsa.
Daman tsawon kwanaki ana ta kus-kus hatta a tsakanin ‘yan jamiyyar ta Democrat a kan lafiyar, sai a wannan karon dan majalisar wakilai na jamiyyarsu, Lloyd Doggett ya yi ta maza ya fito fili yana kira ga shugaban da ya daure, ya hakura da takarar.
Ya ce, bisa la’akari da hadarin da ke tattare da abin da zai iya faruwa, na abin da ya kira kama mulki na wadanda ya kira gungun miyagu masu kama-karya, to ya kamata Biden ya hakura ya ba wa wanda zai iya.
Mista Doggett ya kara da cewa a kodayaushe ya san Mista Biden a matsayin mai Sanya muradun kasa a gaba, yana da kwarin gwiwar cewa zai yanke shawarar janyewa.
Bayan wannan ma sai ga dan takarar kujerar majalisar wakilai na Democrat a mazabar Colarado, Adam Frisch shi ma ya bara da cewa Biden ya ja baya.
To amma da yake magana a wani taron manema labarai shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Amurkar Chuck Schumer, ya ce yana bayan Biden.
Ya ce, ”ina tare da Biden. Mun yi aiki tare tsawon shekara hudu, kuma mun yi wa Amurka aiki sosai da kuma New York ta tsakiya. Ni na Biden ne.’’
To amma daya daya daga cikin dadaddun abokan tafiyar Biden – tsohuwar shugabar majalisar wakilan Amurkar ta Democrat, Nancy Pelosi – ta ce ba a saba wa shari’a ba a nemi sanin kaifin basirar shi kansa Biden da kuma Mista Trump.
Ta yaba da irin dabarar Shugaban, kodayake ta ce a lokacin muhawarar ta ranar Alhamis ya gamu da bacin rana ne.
Da take bayani ga manema labarai a fadar gwamnatin kasar, White House Sakatariyar yada labaran fadar, Karine Jean-Pierre, ta kafe cewa har yanzu Shugaba Biden zai iya aikin da ke gabansa, da tsayawa takarar.
Ta ce, ”mun fahimci damuwar da ake nunawa. Al’amura ba su yi wa shugaban kyau ba a daren, kamar yadda duk kuka sani, kuma da yawanku kun nuna a lokacin muhawarar.
Shugaban, ”ya kamu da mura, muryarsa ta yi gwara-gwara…..”
Da wannan hali da ake ciki, mutumin da ake ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Biden cin zaben fitar da gwani a Carolina ta Kudu, abin da ya kai shi ga samun takarar ta 2020, Jim Clyburn, dan Democrat ya ce zai mara baya ga mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris idan Biden ya ajiye takarar.