Dan Takarar Jam’iyyar Adawa ta Labour ne Keir Starmer yaci Zabe a Kasar Birtaniya
Jam’iyyar Labour ta lashe babban zaben Birtaniya kuma tana kan hanyar samun gagarumin rinjaye.
Tuni Firaiminista mai ci Rishi Sunak na jam’iyyar Conservatices ya rungumi kaddara, tare da taya abokin karawarsa Keir Starmer da zai gaje shi murna.
A jawabinsa na nasara a kwaryar birnin London, Mista Stermer, ya ce bayan shekaru goma sha hudu na mulkin ‘yan mazan jiya, yanzu yan kasar sun rabu da alakakai.
Ya ce ”Kun yi yakin neman zabe, kun kada kuri’a, kun yi zabe, yanzu Allah ya kawo sauyi, don haka canji ya fara nan take”.
Yan Conservatives sun fara sukar juna
A jam’iyyar Conservatives ta Firaminista mai barin gado Rishi Sunak kuwa an fara ce-ce-ku-ce kan gagarumin kayin da jam’iyyar ta sha a zaben.
Wasu fitattun ‘yan jam’iyyar na ƙunƙunin cewa rikicin cikin gida ne ya kayar da su.
Ɓangarorin da ke adawa da juna na ta neman ɗora wa junansu alhaki, sai dai kamar yadda tsohon sakataren tsaron kasar Grant Shapps ya bayyana, jam’iyya ba ta cin zabe sai yayanta sun zama tsintsiya madaurinki daya.
Shi kansa, da karin wasu ministocin gwamnati bakwai sun rasa kujerunsu.
Jagoran jam’iyyar Reform mai ra’ayin kawo sauyi Niger Farage, ya ce siyasar Birtaniya, ta gamu da wani gagarumin juyin waina.