Labaran Duniya

Wasu da Ake Zargin Yan ta’adda ne Sun Sace Daliban Jami’a A Kasar Habasha

Rahotanni daga ƙasar Habasha na cewa wasu mutane ɗauke da makamai sun sace ɗaliban jami’a da dama a yankin Oromia da ke fama da rikici a ƙasar.

Yankin Oromia ya kasance filin fafatawa tsakanin sojoji da ‘yan tawaye.

Daliban na kan hanyarsu ta komawa gda bayan tashi daga makaranta a yankin Amhara na arewacin Habasha, lokacin da masu ɗauke da makaman suka tare su.

Sauran ɗaliban da suka tsakkale rijiya da baya a harin sun ce ‘yan bindigar, sun yi garkuwa da mutane fiye da 100.

Wani da ya ce ‘yar uwarsa na cikin waɗanda aka kama ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun buƙaci a ba su dubban daloli domin a sako ta.

Jami’ar daliban ta ce ta samu rahoton sace ɗaliban amma ba ta bayar da cikakken bayani ba.

Satar mutane domin neman kuɗin fansa ya ƙaru a Habasha.

Hukumomi ba su ce komai ba kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button