Akalla Yan Mata Marayu Sama Da Dari ne Za’a Daura Auren Su A Jihar Zamfara
Ranar Assabar ɗin nan ne za gudanar da ɗaurin auren wasu ƴan mata marayu 105 da suka rasa iyayensu ta dalilin hare haren ƴan bindiga a yankin Bunguɗu da Maru da ke jihar Zamfara, a arewa maso yammacin Najeriya.
Dan majalisar wakilan yankin Abdulmalik Zubairu Bungudu ne ya dauki wannan ɗawainiya, inda ya shaida wa Manema Labarai cewa sai da suka kafa wani kwamitin bincike da ya ƙunshi malamai, sannan aka zaɓo mata biyar biyar daga kowacce mazaɓa da ke yankin don cin gajiyar wannan shiri.
“Mun sanya a nemo ƴan mata 105, waɗanda ba zawarawa ba, duka yan mata, wadanda kuma aka halaka iyayensu sakamakon wannan matsala ta tsaro, waɗanda dukkan su suna da wanda za su aura a ƙasa, kuma an kawo gaɓar da iyaye za su shiga amma babu hali, to a nan ne mu kuma muka shigo, inda za mu ba su kayan ɗaki kama daga kan kujeru, da gado da sauransu, da kuma jarin kama sana’a” inji ɗan majalisar.
Ya ƙara da cewa kafin su amince da aurar da ƴan matan sai da suka shinfda masu wasu ƙaidoji wajen tantancewa, da suka haɗa da cewar lallai sai ta kasance Marainiya, wadda ta rasa iyayenta sakamakon mastalar tsaron da ake fama da ita a yankin, sannan dole ta zama budurwa ba bazawara ba.
Dan majalisar ya ce ”Bayan nan za mu ba wa kowacce amarya jarin Naira dubu dari, yayin da su kuma angwaye za mu basu naira dubu hamsin don su ja jari”
An jima ana gudanar da irin wannan al’ada ta aurar da mutane da dama lokaci guda a jihohin arewacin Najeriya, da zimmar taimaka wa iyayen da ƴaƴansu suka tasa, amma ba su da damar aurar da su, ko da yake wasu na suka a kan cewa wannan ba nauyi bane na gwamnati.
An fi aiwatar da irin wannan shiri ne a wasu jihohi musamman kamar Kano, da Neja da Kebbi, inda a baya aka aurar da daruruwan maza da mata.
Aure, ibada ce mai matukar muhimmanci ga al’ummar arewacin Najeriya wadanda galibinsu musulmai ne, don haka yin sa, na da matukar muhimmanci a wajen su.
Sai dai a lokuta da dama ana zargin ana aurar da ƴan matan da shekarunsu basu kai ba, lamarin da ke janyo suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam.
A baya bayan nan ma an samu rashin jituwa tsakanin ministar mata ta ƙasar Uju Kennedy, da shugaban majalisar dokokin jihar Neja Mohammed Abdulmalik Sarkin-Daji, kan shirinsa na aurar da wasu ƴan mata sama da 100 da aka kashe iyayensu a hare-haren ƴan bindiga lamarin da ya sa har aka je kotu, ko da yake daga bisani an aurar da su.