Gobe ne 1 Ga wata na Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1446
Fadar Sarkin Musulmi ta ayyana gobe Lahadi a matsayin ranar 1 ga watan Al-Muharram na shekarar 1446 bayan Hijirar Annabi Muhammad (S A W).
Cikin wata sanarwa da fadar ta fitar me ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin ganin watan Farfesa Sambo Wali Junaidu ta ce, Sarkin Musulmin kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ya ce yau Asabar ta kasance 30 ga watan Zul-hijja.
Kuma dai Sarkin Musulmin ya sanar da gobe Lahadin a matsayin 1 ga sabuwar shekarar musulunci ne, a sakamakon rashin ganin jinjirin watan a jiya Jumu’a a dukkan sassan Najeriya.
Sanarwar ta buƙaci Musulmin ƙasar su dage da yiwa Najeriya addu’ar Allah ya kawo ƙarshen matsalolin da suka dame ta, harma ya yi fatan Allah ya haɗamu da dukkan alkhairan dake cikin sabuwar shekarar, ya kuma kare musulmin daga dukkan wasu abubuwan ƙi Ameen.