Shugaba Tinubu Na Da Alaƙa Mai Kyau Da Muhammadu Sanusi II – Fadar shugaban Najeriya
Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani game da iƙirari shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano cewa shi ne ke goyon bayan Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero a rikicin masarautar jihar da ake yi tsakaninsa da Muhammadu Sanusi II.
Ɗaya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai, Abdu’aziz Abdul’aziz ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu na da alaƙa mai kyau da duka ɓangarorin biyu “musamman ma Muhammadu Sanusi II”.
Ya ƙara da cewa maganar zargi ne kawai “maras tushe”.
“Abin da mai maganar bai sani ba ko kuma bai faɗa ba saboda siyasa shi ne; shugaban ƙasa na da alaƙa mai kyau da duka waɗanda ke taƙaddama a kan wannan sarauta,” in ji shi.
“Musamman ma Sarki Sanusi II, wanda suke da alaƙa tun lokacin da ya nemi sarautar a 2014. Kuma ya sani cewa Sarki Aminu Ado bai taɓa zuwa ya ga Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa ba tun lokacin da ya hau mulki.
“Amma Sanusi II ya zo ba sau ɗaya ba kuma ya ga shugaban ƙasa. Wannan ya nuna irin alaƙar da ke tsakaninsu. Wani mutum ya fito yana magana a kan wani abu da ba shi da hujja abin takaici ne.”