Shugaba Tinubu yabada damar shigo da Shinkafa, Masara, Alkama da wake na tsawon wata biyar ba tare da haraji ba
Gwamnatin Shugaba Tinubu ta sanar da bayar da umarnin ɓude iyakokin Nijeriya na kan tudu da ruwa domin shigo da wasu kayayyakin abinci ba tare da haraji ba na tsawon kwanakin 150.
Ministan Ayyukan Gona na Nijeriya Abubakar Kyari ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na daƙile hauhawar farashin kayayyakin abinci.
Daga cikin kayayyakin da aka amince a shiga da su ƙasar akwai alkama da shinkafa da masara da wake.
Ga wasu daga cikin jerin matakan da gwamnatin ƙasar ta ɗauka.
Bayar da dama a shigar da kayayyakin abinci na tsawon kwanaki 150 ba tare da haraji ba.
Baya ga kayayyakin da kamfanoni masu zaman kansu za su shigar da su ƙasar, gwamnatin tarayya za ta shigar da tan 250,000 na alkama da metric tan 250,000 na masara.
Gwamnati za ta haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin tsayar da farashi ɗaya da kuma tattara sauran kayayyakin abinci da ke kasuwa domin ajiye su a baitul malin gwamnati.