Labaran Duniya

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Buƙaci Shugaban Kasar Bola Tinubu Ya Shiga Batun Tsada Da Karancin Abinci Dake Addabar Kasar.

Ɗan majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ali Ndume, ya shaida wa Manema Labarai cewa babbar matsalar da ake fama da ita a wannan gwamnati ita ce kofar su a rufe take yadda hatta wasu ministocin ba sa iya ganin shugaban kasa, bare ‘yan majalisa ma su samu zarafin ganawa da shi da bayyana abubuwan da ke faruwa a yankunan da suke.

Sanatan na magana ne jim kadan bayan sun gabatar da wani ƙudurin hadin gwiwa tsakaninsa da takwaransa Sanata Sunday Steve Karimi, suna cewa hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin mutum miliyan 82 za su yi fama da matsalar abinci a Najeriya nan da shekara biyar masu zuwa.

Sanata Ndume ya ce manufar kudurin ita ce, janyo hankalin mahukuntan kasar su san matsalar yunwar da ake fuskanta a Najeriya baki daya, kamar yadda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi, wanda a bana ne aka sanya Najeriya cikin kasasshen da za su fuskanci yunwa a duniya.

”Mun yi da nufin tayar da gwamnati ko tunatarwa idan ba su sa ni ba, su san cewa a cikin Najeriya fa ba wai hauhawar farashin kadai ake fama da shi ba, har da rashin abincin.

Mu na tsoron kar wata rana a tashi ko mutum na da kudin sayan abincin, ya je kasuwa amma ba zai samu ba.

Mun samu labari a jihar Katsina, idan an fara yunwa a kasa kananan yara ne ke fara jin jiki, yara sun fara fama da karancin abinci mai gina jiki, yanayi ne da ke faruwa a wuraren da ake fama da yaki ko fari.

Mun ga yadda ya faru a jamhuriyar Nijar, da Sudan ta Kudu, inda yara ke mutuwa sanadiyyar yunwa, ka ga mun fara ganin hakan a Najeriya,” in ji Ndume.

Ya ce abin da suke son gwamnati ta yi shi ne ta zauna da masana da sauran ‘yan kasa domin sanin yadda za a tunkari matsalar, domin babbar barazanar shi ne a baya gwamnati na tara abinci a cikin rumbunta domin bukatar lokaci irin wannan.

To amma a yanzu babu wannan, ya ce abin ya zama babban tashin hankalin da ake bukatar daukar matakin gaggawa kan hakan.

Wasu rahotanni na cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da za a dauki kwanaki 150 ana shigar da kayan abinci kasar ba tare da biyan kudin haraji ba.

Sai dai Sanata Ndume ya ce; ”Na ga wannan rahoto amma da na bincika, sai na samu cewa gwamnati ta ce ba haka labarin yake ba, ko ta janye, ko ma menene ya kamata a fito karara a gani a kasa.

Abu na biyu kuma duk fa abin da gwamnatin nan ke yi ya kamata a gane gwamnatin jama’a ce domin jama’a, wannan ita ce dimukuradiyya. Ya kamata duk abin da za a yi ya kasance an yi tare da jama’a, su san abin da ake ciki, a tabbatar an kwantarwa da mutane hankali.”

Majalisar Dattijan Najeriyar dai ta nemi gwamnatin kasar ta ɗauki matakin gaggawa kan matsalar tashin farashin abinci da kuma rashin wadatarsa da ke dada jefa talakawan kasar cikin mawuyacin hali.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da ‘yan kasar ke fama da tsadar rayuwa da farashin kayan masarufi musamman kayan abinci, da man fetur wanda yana daya daga cikin abin da ake ganin ya kara tsadar komai a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button