Hukumar NBS tace Jami’an gwamnatoci a Nijeriya sun karɓi Kimanin Naira biliyan 721 a matsayin cin hanci a cikin Shekarar 2023
Aƙalla Naira biliyan 721 ne jami’an gwamnatoci a Nijeriya suka karba a matsayin cin hanci a shekarar 2023, a cewar wani sabon rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasar NBS ta fitar.
Rohoton da hukumar ta fitar ranar Alhamis tare da haɗin gwiwar Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC), ya ce kashi 70 na al’ummar Nijeriya mai mutum sama da miliyan 250 sun ba da cin hanci a lokacin da aka buƙaci su yi haka a shekarar da ta gabata.
A cewar rahoton wanda aka yi wa take da ”cin hanci a Nijeriya: dabaru da ɗabi’a,“ a jimulla, an ƙiyasta cewa an biya kusan Naira biliyan 721 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.26 a matsayin cin hanci ga jami’an gwamnati a ƙasar a shekarar 2023, adadin da ya kai kashi 0.35 cikin 100 na ƙudaɗen ma’aunin tattalin arzikin Nijeriya (GDP).”
Kazalika binciken ya nuna cewa, matsakaicin kuɗin da aka bayar na cin hanci da rashawa ya ƙaru zuwa Naira 8,284, idan aka kwatanta da Naira 5,754 da aka bayar a shekarar 2019.
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa kashi 56 cikin 100 na ‘yan Nijeriya sun yi wata mu’amala da jami’an gwamnatin ƙasar a shekarar 2023 idan aka kwatanta da kashi 63 cikin 100 da aka samu a shekarar 2019.
Sai dai, duk da wannan ragi da aka samu, cin hanci na ci gaba da samun gindin zama, inda kowane mutum da ya bayar da cin hanci ke biyan kaso 5.1, jimullar kusan Naira miliyan 87 kenan a faɗin ƙasar, hakan na nufin an samu ragi daga Naira miliyan 117 da aka ƙiyasta a shekarar 2019.
Haka kuma rahoton ya ce, jami’an gwamnati sun fi neman a ba su cin hanci fiye da wadanda suke aiki a ma’aikatu masu zaman kansu, adadin da ya ƙaru daga kashi 6 cikin 100 zuwa 14 a shekarar 2023.
Duk da wannan ƙari, cin hanci da rashawa a ma’aikatun gwamnati ya ninka sau biyu, fiye da na ma’aikatu masu zaman kansu, in ji rahoton.
Rahotan hukumar ya kuma bayyana cewa kashi 76 na mutanen da suka ƙi ba da cin hancin sun fito ne daga yankin arewa maso yamma, duk da yake alkaluma sun nuna cewar kowanne sashe na kasar ya samu akalla kashi 60 na mutanen da suka ki ba da cin hancin.
”Kashi 95 cikin 100 na cin hancin da aka bayar a Nijeriya, an yi su ne ta hanyar gabatar da tsabar kudaɗe ko kuma aikewa da su ta bankuna,” a cewar rahoton, sannan yawan kuɗaɗen da aka bayar a matsayin cin hanci a shekarar 2023 ya kai naira biliyan 721.
Hukumar ta bayyana cin hanci da rashawa a matsayin matsala ta hudu mafi girma da ya yiwa Nijeriya tarnaki wajen ci gaba a shekarar 2023, baya ga tsadar rayuwa da rashin tsaro da kuma ayyukan yi.
Tuni dai gwamnatin Nijeriya ta ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi da wannan matsala musamman a tsakanin jami’anta wajen kafa hukumomin EFCC da ICPC, sai dai ana iya cewa akwai sauran aiki a gabanta, duk da matakin ɗaure mutane tare da ƙwato dukiyoyin jama’a da suka sace da take ci gaba da yi.
Daga cikin jami’an da waɗannan hukumomi suka yi nasarar gurfanarwa a gaban kotu har da ministoci da gwamnoni da mayan jami’an tsaro da na gwamnati waɗanda da dama daga cikin su suka yi zaman gidan yari ko kuma suke kan can har yanzu.