SERAP Ta Baiwa Gwamnoni Wa’adi Domin Su Mayar Wa Kananan Hukumomi Kudaden Su
Yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan hukuncin da kotun ƙolin ƙasar ta yi na bai wa ƙanann hukumomin ƙasar cin gashin kai wajen kashe kudi, ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta nemi gwamnonin jihohi 36 da ministan babban birnin tarayya Abuja, da su yi lissafi tare da mayar da kuɗaɗen ƙananan hukumomin ƙasar da suka karɓa a baya, ko ta gurfanar da su a gaban kotu.
Kotun ƙolin ƙasar ta ce ci gaba da riƙewa tare da kashe kuɗaɗen ƙanann hukumomin da gwamnonin jihohi 36 da ministan babban birnin kasar ke yi haramun ne.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Kolawale Oluwadare ya fitar, kungiyar ta yaba wa kotun ƙolin kasar kan hukucin da ta yi, da ta ce zai kawo ƙarshen kashe maƙudan kuɗaɗen da ake bai wa ƙanann hukumomin don yi wa jam’a aiki ba bisa ƙa’ida ba.
“Wannan hukucin da kotun ƙolin Najeriya ta yi, ya nuna cewa akwai hukuci, ko dokar da za a iya ammfani da su wajen tuhumar gwamnonin jihohi wajen ganin sun bayar da bayanai kan yadda suka kashe kuɗaɗen ƙanann hukumomin da suka karɓa” a cewar sanarwar.
Oluwadare ya kuma kara da cewar “Hukucin na daga cikin hujojin da za su sa gwamnonin jihohi da ministan Abuja da su bayar da bayanai tare da dawo da kudaɗen ƙanann hukumomin da suke riƙe da su, tare da kashe su ta hanyoyin da ba su dace ba.” inji shi.
Kolawole Oluwadare “bayar da bayanai da mayar wa da ƙanan hukumomi shi ne kawai zai sake dawo da aminci a tsakanin masu riƙe da muƙaman siyasa, tare da ƙarafafa doka.
Idan gwamnoni da gwamnan Abuja, suka gaza bayar da bayani kan kudaden da dawo da ƙudaden ƙanann hukumomin nan da kwanaki 7, SERAP za ta gurfanar da su a gaba kotu, don kare hakkin al’umma” in ji shi.
MR Oluwadare ya kuma ce, tana magana ne don kare haƙƙin al’umma, ya ce gwamnonin da minsitan Abuja za su dawo da ƙannan hukumomin kuɗaɗensu tun daga 1999.
“SERAP din ta ce ba wa ƙanann hukumomin kuɗaɗen su zai taimaka wajen kawar da talauci, tare da bunkasa samar da abubuwan more rayuwa ga yan kasa, tare da inganta harkokin ƙananan hukumomi ta yadda za su tafi yadda ya kamata, musamman sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya dora musu.
“Jihohi 36 da ke Najeriya da babban birnin ƙasar sun karɓi Naira tiriliyan 40 a masatyin kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya da ake ware su don kannan hukumomin ƙasar 774 da ke kasar da Abuja.
A jiya Alhamis ne dai kotun ƙolin Najeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin Mulki, kuma gwamnatin jiha ba ta da ikon naɗawa da tuɓe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi, dole sai ta hanyar zabe.
An dai shafe shekaru, ƙananan hukumomi a Najeriya na ƙarƙashin ikon gwamnonin jihohi ta fuskantar kashe kuɗaɗensu ta hanyar wani asusu da ake kira na haɗin gwuiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi.