An sako ‘yan jaridar Kaduna da ‘yan bindiga suka sace tare da iyalansu_NUJ
Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa, NUJ, reshen jihar Kaduna ta ce an sako ‘yan jaridar nan biyu – Abdulgafar Alabelewe da Abduraheem Aodu – da ‘yan bindiga suka sace tare da iyalansu a jihar cikin makon da ya gabata.
Shugabar ƙungiyar, Asma’u Yawo Halilu ce ta tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.
Asma’u Halilu ta miƙa saƙon godiya ga ofishin kwamishinan ‘yansandan jihar, da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, da babban sifetan ‘yansandan ƙasar, da gwamnatin jihar Kaduna da shugaban ƙungiyar NUJ da kuma sauran al’umma da suka taimaka da addu’o’i har aka kai ga sakin ‘yan jaridar.
To sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin haske kan yadda aka sako ‘yan jaridar ba.
A makon da ya gabata ne dai wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan jarida biyu tare da matansa da ‘ya’yansu a jihar Kaduna.