Al'ajabi
Bikin kamun kifi na Nwonyo a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya.
Bikin kamun kifi na Nwonyo biki ne da al’ummar Ibi ke yi a jihar Taraba a Najeriya.
Tafkin yana da tazarar kilomita 5 daga Arewacin yankin Ibi, biki ne da ake yi duk shekara inda Ibi da makwabtan yankin ke haduwa domin kamun kifi da sake haduwa.
Tafkin dai an ce shi ne mafi girma a yammacin Afirka yayin da yake da tafiyar kilomita 15 zuwa kogin Benue. Sunan Nwonyo yana nufin Ɓoyewa ga manya da haɗari na dabbobin ruwa kamar kada, maciji da sauran su.