Labaran Duniya

Gwamna Abba Ya Bada Naira Miliyan 260 Kashi Na Biyu Na Tallafawa Mata 

A ranar Asabar din da ta gabata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shirin karfafawa mata kashi na biyu tare da raba Naira miliyan 260 ga wadanda suka ci gajiyar shirin. 

Mata 5,200 da aka zabo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar sun samu Naira 50,000 kowacce a cikin wata-wata da nufin inganta kananan hukumomi a jihar. 

Sanarwa daga Sanusi Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun gwamnan ya ce ana zabar mata 100 kowacce daga kananan hukumomi 36 da ke wajen birnin da kuma mata 200 kowacce a cikin kananan hukumomi takwas na manyan biranen kasar a kowane wata don cin gajiyar wannan shirin. 

Da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a gidan gwamnati kafin a raba kudaden, Gwamna Yusuf ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa mata sun dogara da kansu da kuma dogaro da kai, ta hanyar tallafin kudi don kasuwanci da sanin makamar aiki. 

Gwamnan ya bayyana kudurinsa na karfafawa mata gwiwa wajen farfado da saka hannun jari domin inganta tattalin arzikin karkara, bunkasa harkokin kasuwanci da samar da abin alfahari ga wadanda suka amfana. 

Ya bayyana fatansa cewa, da tallafin kudi, wadanda suka amfana za su rubanya kananan sana’o’insu, daga baya kuma za su share fagen bunkasar tattalin arziki tare da karya ka’idar talauci. 

Gwamna Yusuf ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da martaba irin sadau karwar da matan jihar suka yi wajen ganin gwamnatinsa ta kara himma wajen kawo sauyi ga rayuwar mata a jihar Kano.

Sanarwar ta kara da cewa Gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’ummar jihar musamman mata a daidai lokacin da damina ta fara, da su kula da tsaftar muhallinsu domin gujewa cututtuka da kuma kula da tsaftar jikinsu domin samun koshin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button