Labaran Duniya

Rundunar Tsaron Falasdinu Ta Sanar Da Gano Gawarwaki Akalla 60 A Shujaiya

Jami’an tsaron ‘Civil Defence’ ta sanar da gano gawarwakin akalla mutane 60 a karkashin burabuzan da suka rufta da mutane sakamakon kazamin hare haren da sojojin Isra’ila ke kai wa a yankin Shujaiya dake Gaza.

Kakakin rundunar Mahmud Basal ya bayyana haka inda yake cewa sun samo gawarwakin ne bayan janyewar sojojin Isra’ila daga yakin, a wani samame da suka kai tare da jama’ar dake wurin.

A jiya alhamis, Isra’ila tace ta kawo karshen ayyukan da take gunarwa a yankin Shujaiya.

Majiyoyi daga alkahira na bayyana cewar ana ci gaba da tattaunawa da zummar kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin sauran firsinonin da Hamas ke tsare da su.

Bayanai sun ce ana tattaunawar ce tsakanin wakilan Isra’ila da Masar da Amurka da kuma Qatar.

Majiyar Masar tace ana saran tattaunawar ta dora a kan batutuwan da kungiyar Hamas ta amince da su.

Isra’ila tace duk wani shirin tsagaita wuta sai ya kunshi bukatar sakin Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button