Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Yace Babu Wanda ya Isa ya Kore shi a Jam’iyar NNPP
Tsohon gwamnan Kano, kuma jagoran jam’iyyar NNPP na kasa a Najeriya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu su ne halastattun ƴa’ ƴan jam’iyyar kuma sun shigeta ne don samar da kyakkyawar manufa ta ceto Najeriya da ƴan Najeriyar.
Sanata Rabi’u Kwankwason ya shaida wa Manema Labarai hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan ikirarin korar sa daga jam’iyyar ta NNPP da wasu yan jam’iyyar suka ce sun yi, a kwanakin da suka gabata.
Sanata Kwankwaso ya ce babu wanda ke da ikon korar sa daga jam’iyyar da suka raya har ta kai ga matakin da ta kai a yanzu.
“Mu a ganinmu waɗannan mutane ba yan siyasa bane, basu fahimci yadda tsarin yake ba, ni ba shugaba bane kawai na Kano, nine jagoran wannan jam’iyya a Najeriya baki daya, lallai ana son kowa ya shigo wannan jam’iyya, ba za a ce ba a so wani ya shigo ba, wannan jam’iyya ba ta kowa bace” a cewarsa.
Dimukradiyya na da dadi, kuma tana da wuya, a tsari duk lokacin da aka ce hukuma ko jam’iyya ta yi karfi kamar yadda wannan jam’iyya take kankanuwa kafinm mu shigo ta yi karfi a yanzu, muna da sanatoci da yan majalisar wakilai, da gwamna da Rabiu Musa Kwankwaso da Buba Galadima da sauransu, to ka ga dole abubuwa sun sauya daga yadda suke a baya.
Ya kara da cewa sabanin yadda wasu ke yada jita-jita cewar sauyin tambari da jam’iyyar ta yi na da alaƙa da rikicin cikin gida da ta ke fama da shi, Kwankwaso ya ce babu gaskiya da wannan al’amari, domin sun dauki wannan matakin ne duba da yadda suka gamu da matsala wajen gane tambarin jam’iyyar a takarardar kuri’a a zaben da ya gabata.
Kwankwason ya ce “Sababbin kaloli da muka sauya da tutar jam’iyya, da shi kansa kudun tsarin mulkin jam’iyya abu ne da ya da ce da wannn zamani, kuma doka ce ta ba da dama”
Sanata Rabi’u Kwankwason ya ƙara nanata cewa samar sabuwar alamar zai ƙara haɗa kan ƴa’ƴan jam’iyyar tasu.
Dama dai tsagin jam’iyyar NNPP mai mubaya’a ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sanar da korar ƴan kwamitin amintattun da suka dakatar da jagoran jam’iyyar.
Ɗaya daga cikin jigo a jam’iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a wani yunkurin na fasalta al’amuran jam’iyyar.
Shugabancin jam’iyyar dai ya kasu gida biyu, na Legas wadanda sune suka samar da jam’iyyar tun tana jaririya shekaru da dama da suka gabata, da kuma bangaren shugabancin Abuja mai biyayya ga Kwankwaso, wadanda suka raya jam’iyyar bayan shigarsu gabanin zabukan 2023 da suka gabata.