Tinubu Ya Karawa Jihar Kano Mukamai Har Guda Biyu A Cikin Gwamnatin Sa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarawa Jihar Kano Muƙamai guda biyu a ƙarkashin Gwamnatinsa.
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan, ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu a jiya Asabar.
Kuma dai waɗanda Tunibun ya bawa muƙaman sun haɗar da Sanata Bashir Garba Lado a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin majalisar dattawa, da kuma Dakta Baffa Ɗan Agundi a matsayin sabon Darakta-Janar na Cibiyar kula da nagartar ayyuka ta Kasa (NPC).
Bashir Lado dai ya kasance tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, kuma tsohon Darakta-Janar na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar, baya ga gogewar da yake da ita a fannin kasuwanci.
Shi kuma Baffa Babba ya kasance tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar dokokin jihar Kano, kuma tsohon babban magatakarda a babbar kotun shari’a ta jihar, haka kuma tsohon Manajan Daraktan hukumar KAROTA, wanda kuma shine ya riƙe shugaban tawagar matasan yaƙin neman zaɓen shugaba Tinubu a arewa maso yammacin Nigeria a zaɓen da ya gabata.
A ƙarshe Tinubu ya yi fatan zasu yi amfani da ƙwarewar da suke ita wajen sauke nauyin da ya ɗora musu, ta yadda zasu bada tasu gudunmuwar wajen ciyar da ƙasar gaba.