Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Ta Gabatar Da Dan Wasan Faransa Kylian Mbappe
Tauraron dan kwallon Faransa Kylian Mbappe ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar da kulob din Real Madrid na kasar Sipaniya ranar Talata.
“Zan yi matuƙar ƙoƙarina,” in ji Mbappe bayan an gabatar da shi a filin wasa na Santiago Bernabeu.
“#WelcomeMbappé,” in ji kulob din a shafinsa na X, ya kara da cewa an kammala duba lafiyar dan wasan mai shekaru 25.
Bayan sanya hannun, an bai wa Mbappe riga mai dauke da sunansa da kuma lamba 9 da shugaban kungiyar Florentino Perez ya buga a kai.
Mbappe haifaffen Paris ya bar Paris Saint-Germain bayan ya shafe shekaru bakwai. Ya lashe kofin Ligue 1 na Faransa guda shida a cikin shekaru bakwai tare da PSG, kuma ya kasance zakaran Faransa tare da Monaco a 2017.
Ya kuma taimaka wa Faransa lashe gasar cin kofin duniya na 2018 da aka gudanar a Rasha.
Ana danganta Mbappe a daya daga cikin fitattun ‘yan wasa a duniya, inda ci kwallaye 256 a wasanni 308 da ya buga wa PSG a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a kulob din.