Labaran Duniya

Wasu Mahara Sun Harbe Mutun Hudu A Masallaci A Dai Dai Lokacin Taron Ashura

Jami’an Ƴansanda a ƙasar Oman sun ce aƙalla mutum hudu ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a harin da aka kai masallacin Wadi al-Kabir da ke kusa da babban birnin ƙasar Muscat.

Hotunan da aka yaɗa a kafafen sadarwa na intinet sun nuna yadda mutane ke ƙoƙarin tserewa daga masallacin da aka bude wa wuta.

Rahotonni sun ce mutanen sun taru a masallacin ne domin yin taron Ashura, wanda mabiya Shi’a ke yi a Fadin duniya duk shekara.

Ba a cika samun irin wannan rikici a Oman ba.

A gefe guda kuma, Ofishin Jakadancin Amurka ya yi kira ga ƴan ƙasarsa su yi taka tsantsan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button