Labaran Duniya
Dubban ɗalibai a Bangladesh sun yi arangama da jami’an tsaro
Ɗalibai a ƙasar Bangladesh sun sake fitowa kan titunan birnin Dhaka inda suka ƙi bin umarnin haramta zanga-zanga.
Zanga-zangar da suka fara kafin yau ɗin ta jawo mutuwar mutum aƙalla 25 ranar Alhamis.
An tsara yin jana’iza a wurare na musamman da zimmar yin jawabai na tunawa da mutanen da aka kashe.
An sake kashe mutum biyu a yau Juma’a wanda ya sa jimillar mutanen da aka kashe tun bayan fara boren zuwa 33. Sai dai abu ne mai wuya a iya tantance haƙiƙanin mutanen da aka kashe saboda katsewar layukan sadarwa.
Dubban ‘yan ƙasar na zanga-zanga ne saboda matakin gwamnati na rarraba gurbin aiki ga iyalan dakarun sojin ƙasar da suka yi yaƙin neman ‘yancin kan ƙasar a shekarar 1971.