Hukumar Hisbah Ta Lalata Giya Da Sauran Haramtattun ƙwayoyi Da Kuɗinsu Ya Kai Naira Miliyan 60 A Katsina
A wani gagarumin aiki da hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta yi, ta lalata giya da muggan kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 60 a karamar hukumar Funtua.
Aikin ya yi sanadiyar kwacewa tare da lalata kiretin barasa guda 1,750, jarkoki 33 na barasa da aka hada a cikin gida, da wasu haramtattun abubuwa.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito, Kwamandan Hisbah, Dr. Aminu Usman, ya bayyana cewa matakin ya yi daidai da manufar hukumar na kiyaye kyawawan halaye a cikin al’umma. Ya yabawa kwazon jami’an Hisbah, ya kuma bukace su da su ci gaba da taka-tsantsan kan ayyukan su.
Dakta Usman ya yi kira ga malaman addini da su ba su goyon baya, inda ya jaddada cewa kokarin Hisbah ya wuce kowacce kungiya. Ya kuma mika godiyarsa ga Gwamna Dikko Radda bisa yadda yake ci gaba da tallafawa ayyukan hukumar.
Kwamandan Hisbah ya kara da jan hankalin al’umma da su rika kai rahoton wuraren da ake yin lalata, sannan ya yi kira ga iyaye, malamai da shugabannin al’umma da su kara kaimi wajen inganta tarbiyya da kyawawan dabi’u a tsakanin matasa.