Jam’iyyun adawa a Najeriya sun gargaɗi gwamnatin Tinubu kan zanga-zanga
Ƙungiyar gamayyar jam’iyyun siyasar Najeriya ta CNPP ta gargaɗi gwamnati kan yunƙurin rufe bakin masu shirya zanga-zanga a fadin kasar saboda matsin tattalin arziki – da aka shirya yi ranar 1 ga watan Agusta.
Hakan ya biyo bayan zargin da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya yi cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da hannu wajen shirya zanga-zangar.
Jam’iyyun siyasar karkashin inuwar CNPP sun buƙaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta rage kashe kuɗaɗe tare da ɗaukar wasu matakai na samar da ayyukan yi da daƙile tsadar rayuwa, a maimakon anfani da karfi domin toshe bakin talakawan ƙasar.
Batun zanga-zangar dai na cigaba da jan hankalin matasa a shafukan sada zumunta, inda wasu ke cin alwashin fitowa yayin da a gefe guda kuma malaman addini musamman na Musulunci ke cewa ta saɓa ƙa’ida.