Shugaba Bola Tinubu Ya roƙi Yan Nijeriya Su Dakatar Da Shirin Yin zanga-zanga
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya roƙi ‘yan Nijeriya da su janye shirin zanga-zangar da suke niyyar yi a farkon watan Agusta mai kamawa.
Ministan Watsa Labarai na Nijeriya Mohammed Idris ne ya shaida wa manema labarai hakan a fadar gwamnati a Abuja bayan kammala ganawarsa da Shugaban Ƙasar, yana mai cewa Shugaba Tinubu ya nemi masu shirya zanga-zangar da su dakatar da ita su jira su ga matakin da zai ɗauka a kan ƙorafe-ƙorafensu.
Roƙon na Shugaba Tinubu na zuwa ne a yayin da ake ta ci gaba da batun gudanar da zanga-zangar da aka yi wa take da ‘EndBadGovernance’, a fadin ƙasar musamman ma a shafukan sada zumunta.
Lamarin dai ya jawo muhawara ta kowane ɓangare a ƙasar inda wasu ke goyon baya, wasu kuma suna kira da a guji yin “duk abin da ka iya sake taɓrɓarar da yanayin tsaro da dama ake ciki a ƙasar.”
Akwai rahotannin da ke zargin cewa hukumomin tsaro sun fara kama wasu da ake zargin su da hannu a kitsa zanga-zangar.
Minista Idris ya ce “Mun tattauna batun ƙasar gaba daya kuma Shugaban Ƙasa ya bukaci in sake sanar da ‘yan Nijeriya cewa yana sauraronsu, musamman ma matasa da ke kokarin yin zanga-zanga.
“Shugaban kasa ya ce yana sauraronsu kuma yana daukar abin da suke faɗa da muhimmanci; kuma yana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa kasar nan ta yi kyau ba don yau kadai ba har ma nan gaba.
“Kan batun zanga-zangar da aka shirya, Shugaban Ƙasa bai ga buƙatar hakan ba. Ya umarce su da su ajiye wannan tsarin. Ya buƙace su da su jira martanin gwamnati kan dukkan kokensu, ”in ji Ministan.