Labaran Duniya

Yan Bindiga Sun Kashe Wani Jami’in CPG Daya Da Wani Jami’in Sa-kai A jihar Zamfara 

Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai mummunan harin da yayi sanadiyar mutuwar wani jami’in rundunar Askarawan Zamfara da wani ɗan Kungiyar sa-kai a yankin Ƙaura-Namoda da ke jihar Zamfara.

Lamarin dai ya faru ne a daren jiya litinin da misalin karfe 8 zuwa 9 na dare a kauyen Maganin Tandu gundumar Gabake cikin karamar hukumar mulkin kaura Namoda.

Bayan da mutanen suke kan hanyarsu ta komawa kauyen na magami daga Kaura Namoda, kwatsam sai ‘yan bindigar suka yi masu kwantan bauna inda lamarin ya rutsa da Ba’askare mai suna Muhammad Bello da wani jami’in sa kai, inda nan take Suka bakunci lahira.

Haka dai lamarin yake a Sabon Garin Ƙaura Namoda inda ‘yan ta’addan suka Shiga da misalin karfe ɗaya na dare domin kai Hari a garin inda suka samu nasarar yin garkuwa da mutane da dama wadanda har kawo yanzu ba’a iya tantancewa adadin yawan su ba, sai dai kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar ba ta tabbatar da wannan labarin ba.

Shi dai sha’anin tsaro ya zamo karfen kafa a yankunan Zamfara duk da yake hukumomi na furta cewar suna nan suna iya bakin kokarinsu domin kawo karshen Matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button