Labaran Duniya

An Dawo Da Yan Ci-ranin Najeriya Su 158 Da Suka Maƙale A Kasar Libya

Hukumar agajin gaggawa ta NEMA a Najeriya ta ce ta karɓi ƴan ƙasar 158 da suka maƙale a Libya wanda suka sauka a tashar jirgin saman Legas.

Hukumar ta ce sun ƙunshi mata 45 da maza 77 da yara mata 14 da yara maza 12 da kuma jarirai 10 maza da mata, kamar yadda Nema ta wallafa a shafinta na X.

Hukumar ta ce za a ba su horo na koyon sana’o’in hannu bayan kammala tantance su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button