Ana ci gaba Da Aikin Ceto Wadanda Zaftarewar ƙasa Ya Rutsa Dasu A Kasar Habasha
Ana ci gaba da aikin ceto a ƙudancin ƙasar Habasha, yayin da zaftarewar kasa ta yi ajalin mutum akalla 229, tare da fargabar samun ƙarin asarar rayuka.
Tawagar agajin gaggawa da sauran mutane na amfani da shebur da hannaye da jirage marasa matuka wajen neman waɗanda suka tsira da rayukansu a yankin mai nisa na tsaunin Gofa.
Ofishin kula da jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Habasha ya bayar da rahoton cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haifar da zabtarewar kasa a cikin kwanaki uku a jere, tare da nuna damuwa ga kwanciyar hankali da kuma buƙatar kwashe mutum 10,000.
Rashin kyawun yanayin hanya yana hana jigilar manyan kayan aiki da aikic ceto.
Gwamnatin Habasha ta aike da tawagar da za ta mayar da martani ga bala’in, kuma hukumomin agaji na samar da muhimman kayayyakin da ake buƙata.
Mutane 12 ne ke karɓar kulawa a asibiti bayan an ceto su.
Kudancin Habasha dai ya fuskanci ruwan sama mai tsanani da ambaliya kwanan nan.